Matthew 10

Yesu Ya Aiki Sha Biyun

1Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

2Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu: da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗanʼuwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗanʼuwansa Yohanna; 3Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus; 4Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.

5Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa: “Kada ku je cikin Alʼummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa. 6A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Israʼila. 7Saʼad da kuke tafiya, ku yi waʼazi, kuna cewa: ‘Mulkin sama ya kusato.’ 8Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsabtace kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta. 9Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku; 10kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin maʼaikaci ya cancanci hakkinsa.

11“Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi. 12Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa. 13In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku. 14Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku saʼad da kuka fita gidan ko garin. 15Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shariʼa fiye da wannan gari. 16Ina aikanku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.

17“Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majamiʼunsu. 18Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Alʼummai. 19Amma saʼad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa, 20gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.

21“Ɗanʼuwa zai ci amanar ɗanʼuwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ʼyaʼya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 22Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto. 23Saʼad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Israʼila, Ɗan Mutum zai zo.

24“Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa. 25Ya isa wa ɗalibi yǎ zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida, Beʼelzebub,
Da Helenanci Beʼezebowul ko kuwa Beʼelzebowul
me za su ce game da mutanen gidansa?

26“Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yǎ hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa da yardar Ubanku. 30Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

32“Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama. 33Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.

34“Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. Aʼa, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi. 35Gama na zo ne in sa,

“ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,
ʼya da mahaifiyarta,
matar ɗa da surukarta— 
36abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
Mik 7.6


37“Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yǎ zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yǎ zama nawa ba; 38duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yǎ zama nawa ba. 39Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.

40“Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. 41Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci. 42In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”

Copyright information for HauSRK